Daga: Shehu Suleiman Sharfadi
Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya mika gaisuwar fatan alheri ta sabuwar shekara ga Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, Jagoran Jam’iyyar NNPP na kasa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, tare da daukacin jama’ar Jihar Kano, a yayin bikin shiga sabuwar shekara ta 2026.
A cikin sakon sabuwar shekararsa, Kwamared Gwarzo ya bayyana godiyarsa ga Allah Madaukakin Sarki bisa kyautar rayuwa da damar kaiwa ga ganin wani sabon kakar zamani mai cike da zaman lafiya da ci gaban al’umma.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Babban Sakataren yada labaran Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Ibrahim Garba Shuaibu ya sanya wa hannu, wanda aka rabawa manema labarai a Kano.
Kwamared Gwarzo ya jinjinawa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa jagorancin hangen nesa, jajircewarsa kan walwalar al’umma da kuma kokarinsa na dawo da martabar Kano ta hanyar manufofin inganta jama’a da aiwatar da muhimman ayyukan raya kasa.
Haka kuma, ya yabawa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso saboda irin jagorancinsa na tsawon lokaci, basirarsa ta siyasa da kuma irin kulawarsa ta uba, wacce ke ci gaba da zaburar da sabbin shugabanni masu kishin kasa da hidima ga al’umma.
Mataimakin Gwamnan ya sake tabbatar da kudirin gwamnatinsu na ci gaba da kyakkyawan shugabanci, zurfafa ci gaban kananan hukumomi da kuma tabbatar da dai-daito wajen bunkasa bangarori daban-daban a fadin jihar.
Ya kuma bukaci al’ummar Kano da su kasance masu jajircewa, bin doka da oda, tare da ba wa gwamnati hadin kai domin cimma nasarar shirye-shiryen da ake aiwatarwa na canza jihar zuwa matakin cigaba.
A karshe, Kwamared Gwarzo ya yi addu’ar samun sabuwar shekara cike da zaman lafiya, hadin kai, ci gaba da albarka ga jihar Kano da kasa baki daya.




