Shugaban gidan Radio tarayya Pyramid FM dake Kano Dr. Garba Ubale Danbatta ya yi alkawarin hada hannu da Cibiyar Kula da ingantuwar aiyuka ta Ƙasa (National Productivity Centre NPC) domin inganta rayuwar al’umma.
Dr. Garba Ubale Danbatta ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar girmamawa da ya kai wa DG Baffa Babba a ofishinsa.
Da yake jawabi a yayin ziyarar, Dr. Garba Ubale Danbatta ya ce manufar ziyar ita ce gabatar da kansa a hukumance ga Dokta Dan’agundi, kasancewarsa sabon shugaban gidan Radio Nigeria Pyramid FM Kano .

Ya kuma yaba wa Daraktan Janar bisa yadda yake ci gaba da tallafa wa al’ummar jihar Kano ta hanyoyi daban-daban na ƙarfafa tattalin arziki da ayyukan jinƙai, musamman ga malamai, mata, manoma da matasa.
A cewarsa, “Mun zo ne domin gabatar da kanmu a hukumance, tare da nuna godiya bisa gagarumin ƙoƙarin da kuke yi na tallafa wa al’umma ta hanyar ba su tallafi don su inganta rayuwarsu”.
Ya ƙara da cewa Radio Nigeria Pyramid Fm za ta yi amfani da kafarta wajen wayar da kan jama’a game da ayyuka da nasarorin da Cibiyar NPC ke samu.
“Radio Nigeria za ta ci gaba da ba da cikakken labari da yaɗa shirye-shiryen NPC a ƙarƙashin jagorancinku, domin jama’a su fahimta tare da yaba da irin ƙoƙarin da kuke yi,” in ji Danbatta.
Da yake nasa jawabin, Dokta Baffa Babba Dan’agundi ya nuna godiya ga sabon Babban Manajan, tare da yaba masa bisa ƙudirinsa na aiki tare da gidan Radio.
“Ina yaba maka bisa jajircewarka wajen dawo da martabar gidan Radio Pyramid kan matsayin da aka san ta da shi tun lokacin da Gwamnatin Tarayya ta kafa ta, domin amfanin al’umma,” in ji Daraktan Janar.
Ya jaddada muhimmiyar rawar da kafafen yaɗa labarai ke takawa wajen bunƙasa ƙasa, yana mai cewa Radio Nigeria na daga cikin manyan hanyoyin wayar da kan jama’a, ilimantarwa, da kuma isar da manufofi da shirye-shiryen gwamnati ga al’umma.
A yayin ziyarar shugaban gidan Radio Nigeria Pyramid fm ya samu rakiyar wasu manyan jami’an gudanarwa da shugabannin sassa na tashar a yayin ziyarar.