Rasuwar sheikh Dahiru usman Bauchi babban rashi ne ga addinin Musulunci – Shugaban kamfanin Gine Gine na sky Alhaji kabiru sani kwangila yakasai khadimun Nabiyyi.
A madadin daukacin alummar musulmi baki daya Shugaban kamfanin Gine Gine na sky Alhaji kabiru sani kwangila yakasai khadimun yana mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan Sheikh Dahiru Usman Bauchi da al’ummar jihar Bauchi da Najeriya baki ɗaya, bisa rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci wanda ya gudanarda rayuwarsa, wajan yada ilimin addinin musulunci da yiwa alkurani hidima .
A cikin sakon ta’aziyya, da mai taimaka masa a harkokin yada labarai Kamal Yakubu Ali ya fitar , Alhaji kabiru sani kwangila yakasai sky ya roƙi Allah subhanahu wata Ala Ya gafarta wa Sheikh Dahiru usman Bauchi dukkanin kura-kuransa, Ya baiwa iyalansa da danginsa haƙuri da juriya bisa wannan babban rashi.
SKY ya bayyana cewa rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi babban rashi ne ga addinin Musulunci da al’umma baki ɗaya, tare da jaddada cewa Allah Ya sanya Aljanna ta kasance makoma gare shi da sauran alummar musulmi dasu rigamu gidan gaskiya.




