Daga: Ibrahim Sani Gama
Kungiyar Masu Tebura ta Mazan Kwarai Kantin Kwari Ta Nemi Tallafin Gwamnati Don Habaka Kasuwancin Kananan ‘Yan Kasuwa.
Kungiyar masu kasuwancin kayayyaki Sawa ta mazan kwarai dake kasuwar Kantin Kwari a Kano ta bukaci hukumomi da gwamnatoci a matakai daban-daban da su tallafa wa kananan ‘yan kasuwa da jari don habaka harkokin kasuwanci.
Shugaban kungiyar, Alhaji Usman Sulaiman ne ya bayyana haka yayin zantawarsa da manema labarai a ofishin kungiyar dake cikin kasuwar.

Ya ce akwai bukatar gwamnati, musamman ta jihar Kano, ta maida hankali kan kungiyoyin da ke ba da goyon baya a bangaren shugabanci da ci gaban al’umma, inda ya jaddada cewa kungiyar masu tebura ta mazan kwarai na daga cikin irin wadannan kungiyoyi masu kishin kasa.
Alhaji Usman ya kara da cewa lokaci ya yi da gwamnatin jihar Kano karkashin Injiniya Abba Kabir Yusuf za ta tallafa wa wadannan kananan ‘yan kasuwa da jari, domin su ma su more dimokuradiyya kamar yadda ya dace da ‘yan asalin jihar.
A cewar sa, kungiyar ta taka rawar gani wajen ganin kafa wannan gwamnati a lokacin da wasu suka kau da kai, don haka take neman a saka mata da karamci da tallafi.

Haka zalika, shugaban kungiyar ya bayyana yadda kungiyar ke taimaka wa gwamnati wajen karbar haraji ta hanyar fadakar da mambobinta akan muhimmancin biyan haraji da amfanin sa ga al’umma.
Ya kuma ce kungiyar tana taimaka wa membobinta a duk lokacin da wani ya fada cikin matsin rayuwa, ta hanyar tara jari daga cikin mambobinta domin ba da tallafi.
A karshe, ya bukaci mambobin kungiyar da su ci gaba da ba da cikakken goyon baya ga gwamnatin jihar Kano da kungiyar domin ci gaban kasuwanci, al’umma, da jihar baki daya.





