Daga Mustapha Gambo Muhammad

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Ƙasa (EFCC), ofishin shiyar Kano, ta fara haɗin gwiwa da Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA) domin yaki da masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba da sauran manyan laifukan tattalin arziki a cikin Jihar Kano da kewaye.

A cikin wani jawabi da Abubakar Ibrahim Sharada Jami’in Hulda da Jama’a na hukumar Karota ta jihar Kano ya sanya wa hannu ranar litinin ya ce wannan haɗin gwiwa ya samu ne a ranar litinin 13 ga Oktoba, 2025, lokacin da Mukaddashin Daraktan Yankin EFCC, DCP Sa’ad Hanafi Sa’ad, ya kai ziyara ta girmamawa ga Manajan Daraktan KAROTA, Hon. Faisal Mahmoud Kabir, a shelkwatar hukumar dake Kano.

Da yake jawabi yayin ziyarar, DCP
Sa’ad ya bayyana cewa KAROTA na da muhimmiyar rawa da za ta taka wajen dakile ayyukan masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, la’akari da yawan ma’aikatanta da kuma yadda ayyukanta suka bazu a manyan hanyoyi da cikin birni.

Ya roƙi hukumar KAROTA da ta taimaka wajen bibiyar hanyoyin da ake amfani da su wajen jigilar ma’adinai da aka samo ba bisa ka’ida ba, yana mai jaddada cewa irin wannan bayanai na sirri za su taimaka wa EFCC wajen kama da gurfanar da masu laifi waɗanda ke janyo asarar kuɗin gwamnati da lalacewar muhalli.

A nasa jawabin, Hon. Faisal Mahmoud, ya tabbatar da cewa KAROTA tana da cikakken shiri na yin aiki tare da EFCC, yana mai cewa hukumar koyaushe tana marawa baya duk wani shiri da zai taimaka wajen kare tattalin arzikin Jihar Kano.

Ya kuma buƙaci hukumar EFCC ta bayyana a hukumance irin bayanan da take buƙata, tare da tabbatar da cewa KAROTA za ta ba da cikakken goyon baya da duk wasu bayanan sirri da za su taimaka wajen tabbatar da nasarar wannan hadin gwiwa.

← Back

Thank you for your response. ✨

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

ITV Collaborates With Government To Provide Free Tax Education Across Nigeria

By: Mukhtar Yahaya Shehu  A Non governmental organization Independent Tax Volunteers has reiterated…

UNICEF Urges Kano State to Prioritize Child-Sensitive Budgeting

By: Mukhtar Yahaya Shehu  The United nations childrens fund UNICEF says the social…

Ganduje Pushes Garo for Kano Deputy Governor as APC Stakeholders Kick Against Move

By: Mukhtar Yahaya Shehu    The former Governor of Kano State and immediate…

Kano North Journalist Forum Congratulates Comrade Rulwan Idris Malikawa on His Appointment as Board Member, Kano Pillars FC

By: Shu’aibu Sani Bagwai The Kano North Journalist Forum (KNJF), under the…

Speaker condemns killing of 12 travelers in Plateau State ‎

By: Tanimu Salihu ‎ The Speaker House of Representatives Dr. Abbas Tajudeen, has…

Kano Health Ministry Holds iLMD,Data Review Meeting for EDOs, MCH Coordinators Across 44 LGAs

By: Mukhtar Yahaya Shehu  The Kano State Ministry of Health, with support…

WAMY Begins Construction Of Jumu’a Mosques, Plans Borehole Projects in Kebbi

By: Kabir Getso   The World Assembly of Muslim Youths (WAMY) has commenced…

Darma Emerges a New KACCIMA President

By: Mukhtar Yahaya Shehu  Kano Chamber of commerce, industry,mines and Agriculture KACCIMA has…