A Yau Alhamis ne, Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 15, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Sunusi Ado Ma’aji, ta yanke hukuncin kisa ga wasu mutane biyu bayan ta tabbatar da laifin kisan kai akan su.
Hukunci ya biyo bayan shari’ar da ta shafi kisan wani kafinta mai suna Abba Aminu Yalwa a unguwar Danbare, cikin birnin Kano wanda Sagiru Lawan da Abokinsa Kabiru Alaramma suka aikata.
Kotun ta saurari shaidu guda shida daga masu gabatar da ƙara, tare da bayanan kariya daga waɗanda ake tuhuma.
Da yake yanke hukunci Mai Shari’a Ma’aji ya tabbatar da cewar Lauyan gwamnati, Barista Aminu Ado Bello, ya gabatar da ƙwaƙƙwaran hujjoji da suka tabbatar da tuhumar kisan kai akan mutane biyun.
Laifin ya saba da sashe na 221 (B) na dokar manyan laifuka (Penal Code), wanda ke ɗauke da hukuncin kisa.
A shekarar 2018, marigayi Abba Aminu Yalwa ya ba Sagiru Lawan kuɗi, amma daga bisani ya nemi a dawo masa da su. Sagiru ya ce masa ya zo ya nuna masa wani fili a Danbare idan yana da bukatar Siya.
Bayan sun isa wurin, sai Sagiru ya kira abokinsa Kabiru Alaramma. A nan ne suka shake Abba sannan suka caka masa wuka har lahira.
Bayan nazarin shari’ar da cikakken bincike, akan bayanan da shaidu suka gabatar, kotun ta tabbatar da laifin kisan kai kuma ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga Sagiru Lawan da Kabiru Alaramma.