Daga Mustapha Gambo Muhammad
Tsohon direban gidan rediyon Pyramid FM dake Kano Muhammad Sani Aliyu, wanda aka fi sani da Mallam Eleven (11), ya rasu a Babban Asibitin Hadejia, bayan fama da jinya.
Marigayin ya kasance da ne ga Alhaji Salisu Sambajo da Marigayiya Hajiya Kuniniyo, wadda ita ce ‘yar’uwar Alhaji Salisu Sambajo, fitaccen dan kasuwa a Kantin Kwari, Birnin Kano.
Tsohon Shugaban gidan Rediyon Najeriya Pyramid FM, Kuma Shugaban kamfanin sadarwa (Atafi Communications Abuja) Haruna Aliyu Hadejia ne ya sanar da haka a wani jawabi da fitar ta shafinsa na sada zumunta.
Dr. Abubakar Aliyu, Mataimakin Shugaban Babbar Kwalejin Ilimi ta Gumel, Jihar Jigawa, yaya ne ga marigayin.
Tsohon Shugaban gidan Rediyon Pyramid din ya ce Sunan Mallam Eleven (11) ya samo asali ne daga lambar motar haya kirar J5 da ya saba tukawa, mallakar Maigirma Magayakin Hadejia, Alhaji Muhammad Ibrahim Umar Nabagara.
Inda ya ce lambar motar ita ce sha ɗaya (11), wanda ya sa aka fi saninsa da wannan suna.
A cewarsa bayan shekaru da dama yana tuki a cikin rukunin motocin haya, Mallam Eleven ya ci gaba da hidima a matsayin direba a gidan rediyon FM na Pyramid FM, mallakar Gidan Radiyo Nigeria, inda ya shahara da ladabi da biyayya.
Marigayin ya rasu ya bar mata biyu, ‘ya’ya da jikoki da dama.
Shugaban Kamfanin sadarwa Atafi Communications Abuja, Haruna Aliyu Hadeja ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan marigayin, musamman ga kawunsa Alhaji Salisu Sambajo da yayansa Dr. Abubakar Aliyu da Kuma maaikatan Gidan Rediyon Pyramid FM
Ya kuma yi addu’ar Allah ya gafarta masa, ya sada shi da Mala’ikun rahama, ya kuma sanya Aljannah Firdausi ta zama makomarsa. Allahumma amin.
An gudanar da Sallar Jana’iza da Sitira a Hadejia, Jihar Jigawa da misalin karfe 10:00 na safiyar Lahadi.