Daga: Kabir Getso
Rashin tallata aiyukan da gwamnan Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ke yi ne yasa wasu baragurbin ‘yan adawa ke kalubalantar gwamnatin.

-Hon sulaiman muktar madobi
Zababbdn Dan majalissar jaha Mai wakiltar Karamar Hukumar Madobi a zauran majalissar dokoki ta jahar kano, Kuma Dan takarar majalissar tarayyar mai wakiltar kananan hukumomi Kura, Madobi da Garun Malan Hon. Suleiman Muktar Madobi ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a ofishin sa.
Hon. Sulaiman Madobi, yace tun bayan dawowar dimokaradiyya babu wani gwamna a jahar Kano da yayi aikin raya kasa da samar da ingantaccen jagoranci irin Engr. Abba Kabir Yusuf, domin Kano ta dau saiti ta kuma hau gwadaben da ko Abuja wasu aiyukan sai dai ta bi bayan Kano sakamakon samun gwarzon gwamna.

Madobi, ya ce yayi shiri na musamman akan alumomin kananan hukumomin Kura, Madobi da Garun Malan muddin suka sahale ya zama wakilinsu a zauran majalissar wakilai ta kasa.
Daga karshe Dan majalissar yayi kira ga daukacin ya yan jam’iyyar APC dasu guji zabar duk wata jam’iyya wadda ba APC ba, ayi jam’iyya tun dag sama har kasa babu maganar iya linta.